Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar dake Kula da Abinci da Magani, FDA, Ta Amince da Fasahar da Ake Sakawa Jikin Kwayar Magani


Hedkwatar Hukumar dake kula da abinci da magani ko FDA a nan Amurka

Fasahar da ake kira Abilify Mycite zata taimaka wa likitoci da masu bada magani su sani ko marasa lafiya na shan maganinsu akan lokaci

Hukumar dake sa ido kan abinci da magunguna a nan Amurka, ta amince da wata fasahar da ake sakawa a jikin kwayar magani.

Kwayar maganin da ake kira Abilify Mycite a turance, wacce ake amfani da ita wajen warkar da cututtukan da suka shafi tabin hankali, an saka mata wata kwayar na’urar da za ta rika bibiya tare da bai wa likitoci da masu jinya damar gane ko marasa lafiya suna shan magani akai-akai, kamar yadda aka rubuta masu.

“Dabarar bibiyan ko an hadiyi maganin da ake bai wa masu tabin hankali, zai iya taimakawa marasa lafiyan,” a cewar Mitchell Martin, shugaba a sashen kula da magungunan masu tabin hankali da cibiyar yin nazari da bincike kan abinci da magunguna ta FDA.

Ya kara da cewa, “hukumar ta FDA ta amince da amfani da fasaha wajen samar da magunguna, kuma ta himmatu wajen yin aiki tare da kamfanoni, domin a fahimci yadda ilimin fasaha zai iya taimakawa marasa lafiya da masu ba da magunguna.”

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG