Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar dake Kula da Afirka ta MDD Na Neman Hanyar Cigaban Kasashen Yankin Tafkin Chadi da Sahel


Antonio Guterres babban sakataren MDD
Antonio Guterres babban sakataren MDD

Yin la'akari da yadda tattalin arzikin kasashen yankin tafkin Chadi da Sahel ke samun koma baya sanadiyar yawan ayyukan ta'addanci ya sa hukumar dake kula da kasashen Afirka soma neman hanyoyin habbaka tattalin arzikin kasashen yankunan biyu

Lura da yadda harkokin tattalin arzikin kasashen Sahel da Sahara ke fuskantar barazanar durkushewa sakamakon rikicin ayyukan ta'addanci da ake fama dashi a kasashen yankin tafkin Chadi da kasar Mali biyo bayan bazuwar makamai daga kasar Libya ya sa hukumar dake kula da cigaban tattalin arzikin nahiyar Afirka ta fara neman mafitar wannan matsalar da take addabar mazauna karkara.

Almonsur Muhammad wani kusa a kungiyar makiyaya ta KAPAN yana mai cewa ba'a kiwo wuri guda, " a je Mali a dawo, a je Togo a dawo". Yace amma yau akwai matsaloli da yawa saboda ayyukan 'yan ta'adda dake Mali, Nijar, da Chadi. Wannan ya kawowa kiwo cikas ta haka kuma ya shafi tattalin arzikin kasa. Ya cigaba da cewa tattalin arziki baya bunkasa idan ba'a zuwa da dawowa cikin lumana.

Tashin tashinar da Boko Haram ta haddasa na cikin matsalolin da suka fi addabar akalla kasashe hudu a yankin tafkin Chadi.

A kan wannan Sarkin Mene Abdu Kacallu Kachalla Gaso ya bayyana irin koma bayan tattalin arziki da rikicin ya haddasa. Yace koina an samu koma baya walau ta bangaren gwamnati ko zamantakewa ko kuma kasuwanci. Kiwo da noma sun samu koma baya. Sabo da haka ya kira a yi anfani da duk shawarwarin da masana suka bayar a wurin taron. Injishi, da wuya a samu cigaba idan babu zaman lafiya.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG