Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar DPR Ta Rufe Gidajen Mai 20 Saboda Saba Ma Farashin Gwamnati


Wani gidan mai

Sayar da man fetur sama da farashin gwamnati ya janyo rufe wasu gidajen mai a jahar Osun.

Hukumar da ke kula da sayar da man fetur ta kasa, DPR a takaice, ta rufe gidajen mai 20 a jahar Osun saboda sayar da man fetur din sama da farashin gwamnatin tarayyar Najeriya da kuma boye shi.

Mataimakin Shugaban Hukumar ta DPR a shiyyar Ibandan Sadik Ibrahim, ya shaida ma manema labarai a a birnin Osogbo na jahar ta Osun cewa dalilin daukar wannan matakin shi ne a tabbatar kowa na bin umurnin sayar da man bisa farashin da gwamnati ta kayyade.

Shi ma Kwamandan Rundunar Kare Farar Hula (NSCDC) shiyyar Osun wadda ta taimaka wajen daukar wannan matakin, Mr Tajuddeen Balogun ya yi kira ga kowani dan Najeriya da ya bi doka don kowa ya ji dadi hankali ya kwanta.

Ga Hassan Ummaru Tambuwal da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:07 0:00

XS
SM
MD
LG