Hukumar hana zarmiya da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta ce ta kama 'yan damfara, zambar yanar gizo su sha bakwai 17 a kokarin neman mafaka a Kaduna.
Shugaban hukumar a shiyyar Kaduna Mal. Mailafiya Yakubu wanda ya yiwa muryar Amurka karin haske, ya ce hukumar na shawo kan kalubalen da ke kawo cikas a gaban kotunan wannan kasa.
Wanne irin kalubale ke shan gaban hukumar ta EFCC wajen magance cin hanci da rashawa a Najeriya? Malam Mailafiya Yakubu ya ce akwai;
Yaki da cin hanci da rashawa dai na cikin manyan alkawurran gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, sai dai wasu na ganin kawo karshen wannan badakallar aiki ne tukuru saboda yadda ya shiga cikin al'umma ko ta ko ina.
Isah Lawal Ikara ya aiko da wannan rahoton daga Kaduna a Najeriya.
-
Yusuf Harande
Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.