Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kare Hakkin Biladama ta Samu Jami'an Tsaro da Laifin Kisan Kai


Hukumar Kare Hakin Biladama
Hukumar Kare Hakin Biladama

Idan ba'a anta ba bara ne jami'an tsaro a Najeriya suka farma wani gida a anguwar Apo dake cikin Abuja suka kashe wasu matasa takwas suka kuma raunata wasu da sunan cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Bara ne jami'an tsaron Najeriya SSS da sojoji suka farma wani gida da ba'a gama gininsa ba inda wasu matasa ke fakewa suka kashe matsan takwas kana suka raunata wasu da zargin cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Kashe matasan ya jawo cecekuce da tada jijiyoyin wuya domin jama'ar kasar da dama basu yadda da ikirarin jami'an tsaro ba. Bugu da kari wasu 'yanuwan wadanda aka kashe sun fito suna karyata batun. Ban da haka kunyiyar keke napep ta kalubali jami'an tsaro inda tace wadanda aka kashe 'ya'yan kungiyarta ne kuma har ta nuna katunan shaida nasu.

Kungiyar keke napep ta dauki lauya domin ya taimaketa. Haka ma ita hukumar kare hakin biladama ta gudanar da bincike mai zurfi. Chidi Odinkalu shugaban hukumar ya bayyana sakamakon binciken. Yace hukumar bata samu matasan da laifi ba. Saboda haka samamen da jami'an tsaro suka kai ya keta hakinsu lamarin da ya kaiga rasa rayuka takwas da raunata goma sha daya. Ya nemi a biya diyar nera miliya goma goma ga duk wadanda aka kashe kana a a biya nera miliyan biyar biyar ga wadanda aka raunata.

Usman Buba Goza shugaban kungiyar keke napep a Abuja yace ya fi kowa farin ciki da hukuncin domin sun nemi gwamnati ta daina kiransu 'yan Boko Haram kuma hakan ya faru. Shi ma Barrister Solomon Dalung lauya mai kare hakin biladama yace hukuncin ya kwantar masa da hankali. Yace an yi adalci. Yace yanzu an kama hanyar kwatarwa jama'a hakinsu daga jami'an SSS.

Ga rahoton Medina Dauda.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG