Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kare Hakkin Bil Adama Ta koka Akan Yadda Tace Anyi Jifar Matattar Mage Da ‘Yan Gudun Hijira.


Najeriya 'yan gudun hijira a Nijar, Mayu 6, 2015.

Shugaban hukumar yace abin takaici ne ma’yan gudun hijirar sun shafe fiye da shekara guda amma babu taimakon kuzo ku gani da gwamnatin jihar ke basu.

Daga nan sai ya bukaci ‘yan gudun hijirar su kwantar da hankular su.Ga abinda yake shaida musu.

‘’Yanzun abin da gwamnati keson yi muku shine ta gina muku gidaje sabbi, idan kun koma zaku je ku zauna a ciki ne, da yawan ku da aka kone muku gidaje yakamata gwamnati ta gina muku wasu gidaje ne’’

Sai dai kuma a waje daya gwamnatin jihar ta mayar da martini game da wannan sukan da hukumar kare hakkindan adam din take yi mata na rashin kulawa da ‘yan gudun hijirar.

Mr Anthony Dan Buran dai shine kwamishinan yada labarai na jihar Taraban ga kuma abinda yake cewa.

‘’Kokawan nan da suka yi basu kyautata muna ba, duk abin nan da muke bayar suce sun koka, to sun koka kamar yaya? Ko kunji cewa gwamnatin tarayya ta baiwa jihar Taraba gudun mowa ne abasu bata basu ba? Ya kamata idan ana sara to a rika duba bakin gatari, domin mu muna bakin kokarin mu a matsayin mu na gwamnati muna taimaka musu, muma muna rokon gwamnatin tarayya tazo ta dubi yanayin da wadannan mutanen suke ciki, su dan kara taimako akan wanda jihar Taraba take yi wa wadannan mutanen’’

Kawo yanzu dai dubban ‘yan gudun hijira ne ke warwatse a ciki da wajen jihar kamar yadda wakilin sashenHausa na VOA Ibrahim Abdul Azeez yace ya gane wa idanun sa, a garin Bantaje.

Ga Ibrahim Abdul AZeez din da ci gaban bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG