Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwallon Kafa Ta Duniya, FIFA, Ta Dakatar Da Najeriya


Najeriya da Girka a wasan cin kofin duniya a Afirka ta Kudu
Najeriya da Girka a wasan cin kofin duniya a Afirka ta Kudu

Dakatarwar tana nufin cewa Najeriya ba zata iya buga wasan share fagen cin kofin Afirka ranar lahadi da kasar Guinea kamar yadda aka shirya ba

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta dakatar da Najeriya daga shiga duk wata gasa ta kasa da kasa a saboda yadda gwamnati take katsalanda a harkokin kwallon kafa a kasar.

Wata sanarwa ta ce Kwamitin Gaggawa na hukumar FIFA ya cimma wannan shawara jiya litinin, a bayan wasu abubuwan da suka faru ga hukumar kwallon kafa ta Najeriya cikin ‘yan kwanakin nan. Kwamitin yace wadannan abubuwa sun hada da matakan da kotu ta dauka kan wakilan kwamitin zartaswar huikumar kwallon kafar Najeriya, da matsin lamba kan a kori mai rikon mukamin sakatare janar na hukumar da kuma shawarar a koma ga wasannin lig-lig na kasa ba tare da an saukar da kulob-kulob da suka zo na karshe daga babban rukuni ba.

A watan Yuli ma, hukumar ta FIFA ta yi barazanar dakatar da Najeriya a bayan da shugaba Goodluck Jonathan yace zai haramtawa kungiyar Super Eagles ta kasar shiga duk wata gasa a kasar waje na tsawon shekaru biyu.

Wannan dakatarwa da hukumar FIFA ta yi jiya litinin, tana nufin cewa ba za a kyale Najeriya ta buga wasa da kasar Guinea kamar yadda aka shirya ranar lahadi mai zuwa ba a zagaye na biyu na wasannin share fagen cin kofin Afirka. A lokacin wannan dakatarwa, Najeriya ba zata iya shiga duk wata gasar kwallon kafa ta yanki ko ta nahiya ko ta duniya ba, ciki har da wasanni na kulob-kulob da wasannin sada zumunci. Haka kuma, babu wani wakili ko jami’I na hukumar kwallon kafar Najeriya da zai iya cin moriyar duk wani shiri ko kwas ko horaswa da hukumar FIFA ko kuma Hukumar Kwallon kafar Kasashen Afirka zasu shirya.

XS
SM
MD
LG