Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwastam Ta Cafke Miyagun Kwayoyi Har Na Naira Miliyan 400 A Najeriya


Ganyen Tabar Wiwi
Ganyen Tabar Wiwi

Hukumar kwastan mai yaki da fasa kwauri ta kama miyagun kwayoyi nau’in tabar wiwi na kusan Naira Miliyan 400 a cikin watanni shida na wannan shekarar, wanda ake niyyar shigowa dasu Najeriya.

A wani taron manema labarai da hukumar ta Kwastam dake kula da iyakokin Najeriya, ta nuna cewa ana shigowa ne da tabar wiwi daga kasar Ghana. A cewar Alhaji Yusuf Umar dake zama kwantirola mai kula da shiyyar gabar ruwan yammacin Najeriya, yace a shekaran jiya ma sun kama wasu miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai Naira Miliyan ‘daya da Talatin.

Hukumar kwastan ta bayyana cewa zata tashi tsaye wajen ganin ta kare kan iyakokin Najeriya, musamman ma ganin yadda ake zargin wasu ‘yan tsagera da neman tayar da rikici a kasar na ganin ba a ayi amfani da kan iyakokin Najeriya ba wajen shigowa da makamai kasar ba.

Shugaban hukumar kwastam mai kula da ruwan yammacin Najeriya, ya bayyana cewa nan gaba kadan za a samu wasu sabbin kayan aiki, da suka hada da jirage masu shawagi don taimakawa wajen yin sintiri a fadin kasar.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG