Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwastan Ta Kama Wasu Kaya Da Yawa Akan Iyakar Lagos Da Janhuriyar Benin


Shugaban Hukumar Kwastam Reshen Tashar Ruwa Ta 'Tin Can' A Lagos
Shugaban Hukumar Kwastam Reshen Tashar Ruwa Ta 'Tin Can' A Lagos

Hukumar Kwastam tayi kira ga mazaunan da ke kan iyakokin Najeria da su baiwa hukumar hadin kai wajen dakile harkokin yan fasakwauri a kasar, inda ta bayan cewa ta kama haramtattun kayan fasakwauri na Naira Biliyan 12.

Hukumar Kwastan ta Najeriya ta kama haramtattun kayan fasakwauri na kimanin Naira Biliyan 12 a yan watannanin baya akan iyakan Najeriya da Jamhuriyar Benin.

A wani taron da hukumar kwastam ta gudanar a yankin Seme ta bayana kayakin da ta kama da suka hada da kajin kankara, da buhunan shinkafa da kayyakin atamfofi da shaddodi. Hukumar tayi kira ga mazauna kan iyakokin Najeriya da su cigaba da baiwa hukumar gudumuwar da ya dace wajen dakile harkokin yan fasakwauri a kasar.

Kwantrola Muhammad Jibril ya bayyana cewa an hana shigowa da shinkafa ta iyaka sai ta tashar ruwa, ya kara da cewa manyan motocin da ke dauko shinkafa basa bin hanyar Seme inda ya bayyana cewa shinkafar da suke kamawa ta kananan motoci ake shigowa da su.

Hukumar Kwastam ta dauki matakai na fitar da man fetur daga Najeriya zuwa manyan kasashe, wanda hukumar ta ce tana taimakawa zagon kasa wajen tattalain arziki da kuma haifar da karancin man fetur a Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG