Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwastan Najeriya Reshen Jihohin Osun da Oyo Ta Tara Biliyoyin Nairori


Ministar Kudin Najeriya, Kemi Adeosun, da hukumar kwastan ke karkashinta

Hukumar kwastan dake kula da jihohin Osun da Oyo ta tara biliyoyin Nairori a tsakanin watan Janairu da Nuwamba na wannan shekarar

Cikin watanni goma na wannan shekara hukumar kwastan Najeriya dake kula da jihohin Osun da Oyo ta tara wa gwamnatin tarayya biliyoyin Nairori.

Alhaji Abdulsalam Hassan mukaddashin kwantrolan hukumar dake kula da jihohin Osun da Oyo yace tsakanin watan Janairu da Nuwamba na wannan shekarar 2015 reshen ya tarawa gwamnatin tarayya kudi Naira biliyon 13 da miliyan 201 da 987, 322.77.

Hakazalika babban jami'in kwastan din yace ta bayanan leken asiri sun gano wani kungurmin daji inda suka kama manyan motoci biyar dake shake da buhuwan shinkafa da kudinsu ya kai Naira miliyan 23 da 915, 998. Yace hukumar ba zata yi kasa a gwuiwa ba wajen sanya kafar wando daya da duk wanda ya taka dokar shigowa da kaya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:00 0:00

XS
SM
MD
LG