Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar kwastan ta jihar Oyo ta kama wasu motoci shake da tabar wiwi


Kunshin miyagun kwayoyi irin su tabar wiwi

Jami'an hukumar kwastan ta Najeriya dake kula da jihohin Oyo da Osun sun kama wasu motoci shake da tabar wiwi da tufafin gwanjo amma sun mika tabar ga hukumar dake ta'arnaki da sha ko fataucin miyagun kwayoyi ko NDLEA a takaice.

Mr. Ogunkoya kwanutrolan hukumar kwastan dake kula da jihohin Oyo da Osun shi ya mika tabar ga jami'an NDLEA.

Yace sun samu nasarar gano miyagun kwayoyin ne saboda yin anfani da leken asiri da tara bayanan siri da jami'ansa suka yi.

Kwanturolan ya ja kunnuwan masu fasakwauri a jihar Oyo yace ya fada ya kuma kara jaddadawa babu damar yin sumoga a jihar.

Yayinda take karbar tabar kwanturolar NDLEA ta jihar Oyo tace dama hukumar kwastan da NDLEA Danjuma ne da Danjummai. Tace yayinda take nata aikin idan ta kama 'yan sumoga zata mikawa hukumar kwastan.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00

XS
SM
MD
LG