Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwastan Ta Lalata Buhuhunan Shinkafa 2000 A Yankin Lagos


Buhuhunan shinkafa da hukumar kwastan ta kama a kudu maso yammacin Najeriya
Buhuhunan shinkafa da hukumar kwastan ta kama a kudu maso yammacin Najeriya

Daga cikin buhuhunan shinkafa dubu 12 da hukumar kwastan ta kama a kan iyakar Seme ta lalata dubu biyu da suka lalace

Buhuhunan shinkafa dubu biyun da hukumar kwastan ta lalata na cikin kimanin buhuhuna dubu 12 da ta kama a 'yan watannin nan.

Shugaban hukumar ta kwastan dake kula da iyakar kasa ta Seme Kwanturola Muhammad Aliyu na yankin Badagry ya shaidawa Muryar Amurka a wani taro na manema labarai. Injishi ga wanda bai sani ba shinkafar ta dade a ajiye har ta lalace.

A cewarsa idan sun kama shinkafa su kan duba su ga mai kyau da mara kyau domin su waresu daban. Ita mai kyau ita ce ake kaiwa sansanin 'yan gudun hijira domin a taimaka masu.

Mara kyau sai su gayawa Abuja domin ba da shawara. Sai a gaya masu su kira hukumar dake kula da abinci da abun sha wato, NAFDAC. Sakamakon binciken da ita hukumar NAFDAC ta aiwatar ya nuna ko dabba ma bai kamata ya ci shinkafar ba balantana mutum.

Mr. Sunday Ona Oche mataimakin darakta na hukumar NAFDAC su ne suke taimakawa wurin binne gurbatacen abinci, ko abun sha ko magani. Ya kara dacewa tare da hadin gwuiwar kwastan da sauran mahunkumta dake yankin suna tafiyar da ayyukansu kamar yadda ya kamata domin hana shigowa da haramtattun kaya musamman abinci da kwayoyi ko magunguna.

Sai dai mutanen dake zaune a yankin sun dauka yin sumoga hakkinsu ne dalili ke nan da suke yakar hukumar kwastan da makamantansu.

Baicin shinkafa hukumar kwastan ta kama motoci dankare da atamfofi. Kodayake shigowa da atamfa ba laifi ba ne amma sai an biya haraji.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG