Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Lafiya Ta Duniya Ta Cika Shekaru 70


Darekta Janar na Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus a wani taro da ya halarta a birnin Geneva
Darekta Janar na Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus a wani taro da ya halarta a birnin Geneva

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta cika shekaru 70 da kafuwa, inda ta kwashe shekaru da dama tana yaki da cututtaka da ke addabar duniya, amma duk da wannan nasara, masana na ganin har yanzu akwai jan aiki a gaban hukumar.

Yau bakwai ga watan Afrilu, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta cika shekaru 70 da kafuwa, sannan rana ce har ila yau da aka ware a matsayin ranar Lafiya ta Duniya.

Hukumar ta WHO, ta jagoranci ayyuka daban-daban na yaki da cututtuka masu saurin kisa, kamar irinsu bakon dauro.

Sannan ta hada kai da sauran sassan Duniya domin yaki da sauran cututtuka da suka hada da cutar shan-inna ta Polio, inda a bara bayanai suka nuna cewa yara 17 ne kadai suka kamu da cutar a duk fadin Duniya.

Sai dai bayanai na nuni da cewa hukumar ta fuskantar kalubale da dama.

Rahotannin sun nuna cewa samun alluran rigakafin cututtuka a wasu yankuna na Duniya ya zama babban kalubale, lamarin da ya sa aka sa taken wannan shekara a matsayin “Health for All” wato samar da Lafiya ga “kowa da kowa.”

“Kusan irin kalubalan da muke gani a ko ina, na da nasaba da yanki, wato wuraren da ake fama da rashin isassun cibiyoyin kiwon Lafiya, ko kuma matsalolin da ke da nasaba da irin tsawon jiran da mutum zai yi kafin ganin likita da kuma rashin isassun likitocin.” Inji James Fitzgerald, jami’i a hukumar ta WHO.​

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG