Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Lafiya Ta Duniya Tana Kokarin Kawar da Gubar Dalma


Kwararrun lafiya a Najeriya su na binciken cutar gubar dalma

Hukumar lafiya ta duniya tace gubar dalma tana da hatsarin gaske musamman ga kananan yara.

Hukumar lafiya ta duniya tace gubar dalma tana da hatsarin gaske musamman ga kananan yara. Hukumar lafiya tayi kokarin fadakarwa game da wannan cutar a makon shawo kan dafin dalma na duniya da aka yi da taken – ‘yantattun yara domin rayuwar lafiya ta nan gaba.

An kiyasta cewa mutane 143,000 ke mutuwa kowacce shekara ta dalilin dafin dalma. Haka kuma gubar dalma take da alhakin kamuwa da rashin lafiyar kwakwalwa na kimanin kananan yara dubu 600,000 yawanci ana samun gubar ne daga fenti.

Hukumar lafiya ta duniya tace gubar dalma ce kimanin kashi 10 cikin dari na cututukan da ke ake dauka ta sinadari. Wannan ta zama babbar matsala ganin yadda yake shafar kananan yara da kuma sa mutuwar jinjirai. Yana kuma shafar manya wajen aikinsu, wannan yafi yawa a kasashe masu tasowa.

Gubar dalma ta kasance matsala a kusan dukan kasashen duniya kasancewa har yanzu ana amfani da fenti mai gubar dalma. Matsalar tana kara yawa saboda sababbin gine gine da kuma gyare gyare da ake yiwa tsofaffin gine gine ko makarantu. Wannan kuma yana faruwa a kasashe da dama.

Ana daukar gubar dalma ba tare da an sani ba saboda ba a iya ganinta da ido. Idan gubar dalma tayi yawa a jikin mutum tana iya sashi kamuwa da cutar da ba za a iya warkarwa ba musamman a cikin kananan yara. Gubar dalma tana sa kananan yara su zama dakikai. Manya sau da dama suna daukar gubar dalma wajen aikin da ya shafi taba ruwan batir ko shaker fenti. Yana sa cutar koda da kuma hawan jini.

Hanya daya da kasashe zasu rage yaduwar gubar dalma, itace ta hana amfani da ita a fetir daukar wannan matakin ya taimaka wajen rage illar gubar dalma a duniya gaba daya. Wannan wani abu ne dake karfafawa da kuma tabbatar da wannan zai kawar da dalma – kuma mataki na gaba shine kawar da fentin dalma, wanda ake gani zai taimaka matuka.

Kawo yanzu kasashe talatin sun shawo kan matsalar gubar dalma baki daya. Hukumar Lafiya Ta Duniya da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar hadin kai ta duniya kan yaki da gubar dalma suna kokarin ganin an sami a kalla kasashe 70 da suka shawo kan gubar a shekara 2015.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG