Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar USAID Ta Ware Dala Miliyan 4.9 Don Aikin Raya Ilimi A Najeriya


USAID

Hukumar raya kasashe ta Amurka USAID ta ware kudi har Dala Miliyan 4 da Miliyan 900 don aikin raya ilimi a jihohin Najeriya 36 da Abuja.

Shugaban hukumar USAID a Najeriya, Michael Harvey, yayi bayani bayan rattaba hannu da gwamnatin Najeriya tayi kan yarjejeniyar raya ilimi a kasar. Bisa ga rahotan hukumar kididdiga ta Najeriyar da ta gano an sami karuwar mata dake shiga makarantu musammam ma a jihohin Arewa.

Mr. Harvey ya nuna farin ciki da yadda yace yayi ran gadi a yankunan arewa inda yaga a wasu guraren Masallatai da Majami’u na samar da waje da akan kafa makarantu, don samawa yara saukin samun ilimi. A cewar Mr. Harvey, “Mu wannan hukumar muna da tsarin kafa wasu yan cibiyoyi masu shigen makarantu a cikin al’umma, da zamu dauki nauyinsu don tabbatar da ilimin ya shiga dukkan lunguna.”

Shugaban hukumar ilimin bai daya na Najeriya, Dakta Sule Dikko, shine ya wakilci ma’aikatar ilimi a wajen yarjejeniyar, da yace ta hanyar bin tsarin kididdigar za a cimma gagarumar nasara.

A nasu bangaren malaman addinin islama na kara taimakawa wajen karfafa ilimin Boko a matsayin halal, don yaki da akidar Boko Haram.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG