Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Yaki Da Fataucin Miyagun Kwayoyi A Nijar Ta Kama Wasu Diloli Dauke Da Kwayoyi Na Daruruwan Miliyoyin CFA

Hukumar Yaki Da Fataucin Miyagun Kwayoyi A Nijar Ta Kama Wasu Dilloli Dauke Da Kwayoyi Na Daruruwan Miliyoyin cfa
Hukumar Yaki Da Fataucin Miyagun Kwayoyi A Nijar Ta Kama Wasu Dilloli Dauke Da Kwayoyi Na Daruruwan Miliyoyin cfa

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Jamhuriyar Nijar ta kama wasu mutune dauke da kwayar da aka shigo da ita daga Indiya da nufin sayar da wani bangarenta a mahakar zinaren jihar Agadez yayinda ake hasashen yiyuwar shigar da dayan bangaren kasar Libya.

NIAMEY, NIGER - Kwayoyin tramadol samfarin Royal kimanin 339,364 da kwayoyin EXOL da ake kira farin malan kimanin 8,000 ne hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi wato OCRTIS ta gabatar wa manema labarai wadanda ta ce jami’anta sun kama a hannun wasu mutane 5 dukkansu ‘yan Nijar bayan gudanar da binciken da ya kai su kauyen Yaboni da ke kewayen birnin Yamai.

Hukumar Yaki Da Fataucin Miyagun Kwayoyi A Nijar Ta Kama Wasu Dilloli Dauke Da Kwayoyi Na Daruruwan Miliyoyin cfa
Hukumar Yaki Da Fataucin Miyagun Kwayoyi A Nijar Ta Kama Wasu Dilloli Dauke Da Kwayoyi Na Daruruwan Miliyoyin cfa

Hukumar ta kuma gabatar da motoci 3 da babura 2 hade da zunzurutun kudi miliyan 5 da ‘yan kai na CFA da wasu kayayyaki na daban wadanda tace ta kama a hannun wadannan masu safara.

Mataimakin alkali mai kare muradan gwamnati a babbar kotun birnin Yamai substitu du Procureur Boubacar Amadou Souleymane, ya yaba da wannan aiki da ke bukatar samun goyon bayan al’umma da gwamnatin Nijar.

Hukumar Yaki Da Fataucin Miyagun Kwayoyi A Nijar Ta Kama Wasu Dilloli Dauke Da Kwayoyi Na Daruruwan Miliyoyin cfa
Hukumar Yaki Da Fataucin Miyagun Kwayoyi A Nijar Ta Kama Wasu Dilloli Dauke Da Kwayoyi Na Daruruwan Miliyoyin cfa
Hukumar Yaki Da Fataucin Miyagun Kwayoyi A Nijar Ta Kama Wasu Dilloli Dauke Da Kwayoyi Na Daruruwan Miliyoyin cfa
Hukumar Yaki Da Fataucin Miyagun Kwayoyi A Nijar Ta Kama Wasu Dilloli Dauke Da Kwayoyi Na Daruruwan Miliyoyin cfa

Duk da matakan da hukumomi ke dauka don kara zuba ido akan hanyoyin zirga-zirga, fataucin miyagun kwayoyi wani al’amari ne da ke kara tsananta a ‘yan shekarun nan a Nijar, abinda ke nunin bukatar kara maida hankali wajen ayyukan fadakarwa, a cewar Idrissa Amadou sakataren kungiyar LCDJ kariyar matasa.

Safarar miyagun kwayoyi wani babban laifi ne da dokokin Nijar suka tanadi hukunci akan dukkan wanda aka kama da hannu a ciki, inda a kan iya kulle mutun a kurkuku daga wata 1 zuwa shekara 1 ko shekaru 10, har zuwa shekaru 30, bisa ga girman laifin da mutun ya aikata.

Saurari rahoton cikin sauti:

 Hukumar Yaki Da Fataucin Miyagun Kwayoyi A Nijar Ta Kama Wasu Dilloli Dauke Da Kwayoyi Na Daruruwan Miliyoyin cfa.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00
XS
SM
MD
LG