Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar EFCC Ta Gana da Masu Sharhi a Kafofin Sadarwar Zamani


EFCC
EFCC

Aci gaba da kokarin wayar wa mutane da kai, Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Nigeria, hukmar tayi wata ganawa da masu rubuce-rubuce a kafofin sadarwan zamani

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Nigeria Zagon kasa ta Nigeria ta gana da marubutan hanyoyin sadarwa ta zamani a Abuja.

Shugaba hukumar Ibrahim Magu yace sun shirya wannan taro ne domin yaki da cin hanci da rashawa abu ne dake bukatar gudunmuwar ko wane dan Nigeria.

Yace bai kamata ace an bar wa hukumar kashin mahaukacin kare ba, yace jama’ar kasa da yawa na anfani da wannan hanyoyin sadarwan ta zamani.

Da aka tambaye shi ko yaya yaji da tambayoyin da mahalarta taron suka yi masa, sai Magu yace wannan shine ya dace domin ta haka ne zasu kara sanin ayyukun hukumar.

Shugaban hukumar ta EFCC yace ba zasu yi kasa a gwiwa ba har sai sunga abinda ya ture wa buzu nadi wajen yakar akidar cin hanci da rashawa a Nigeria, musammam da yake suna samun cikakken goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Ga Sale Shehu Ashka da Karin bayani: 2'52

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG