Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar 'Yansandan Jihar Gombe Ta Hana Hawan Babura har Na Tsawon Kwana Hudu


Hayaki ya tashin inda dan kunar bakin wake ya tarwatsar da kansa jiya a Gombe.
Hayaki ya tashin inda dan kunar bakin wake ya tarwatsar da kansa jiya a Gombe.

Daga jiya har Talata mai zuwa hukumar yansandan Gombe ta hana hawan babura biyo bayan tashin bama-bamai

A wata sanarwa da hukumar ta bayar a rubuce tace daga daya ga wannan watan har zuwa hudu ga watan ta hana hawan babur kowane iri ne a garin Gombe.

Sanarwar ta samu sa hannun kakakin hukumar wato DSP Kwaja Attajiri inda yace yin hakan ya biyo bayan tashin bama bamai a wurare biyu da suka hallaka 'yan kunar bakin waken dake dauke dasu.Kakakin yayi karin bayani da shirin da su keyi na tarbar manyan baki biyu a garin.

Lamarin ya faru ne daidai da lokacin da ake cewa shugaban kasa zai isa garin. Kakakin 'yansandan yace shirin zuwan shugaban kasan yana nan ba'a dageshi ba. Shugaban kasa mai ci yanzu zai ziyarci garin yau kana tsohon shugaba wato Buhari shi ma ya isa garin jibi.

Ya kira jama'a kada su yadda wasu su batasu domin mutanen jihar Gombe mutane ne masu son zaman lumana.

Dangane da tashin bama baman Attajiri yace an fara bincike kuma zasu shaidawa jama'a abun da bincikensu ya gano

Wani ganao yace akalla mutane uku ne suka mutu tare da wani mai sayar da rake.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG