Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zaben Afghanistan Na Fargaban Rashin Tsaro Na Iya Hana Mutane Fitowa Zabe


Wurin da aka kai harin kunar bakin wake a Kabul lamarin da ya tsorata hukumar zaben kasar

Biyo bayan harin da ya hallaka mutane 57 tare da jikata wasu 100 a Kabul hukumar zaben kasar Afghanistan ma fargaban cewa mutane zasu kauracewa zabe

Bayan da wani dan harin kunar bakin wake ya halaka mutane 57 ya kuma raunana wasu fiyeda da dari a birnin Kabul, hukumar zaben Afghanistan mai zaman kanta tana fargabar cewa rashin tsaro zai karya wa mutane guiwar fitowa domin zaben 'yan majalisa dana kananan hukumomi.

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai harin a jiya Lahadi, a wata cibiyar rarraba katin sheda, inda daruruwan mutane suka hallara domin su nemi katin saboda zaben kasar mai zuwa.

Mukaddashin shugaban hukumar zaben kasar Maazullah Dawlati, yace rashin tsaro zai kashe guiwar masu kada kuri'a, lamari da zai kassara tsarin na tafarkin demokuradiyya.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG