Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zaben Nigeria, INEC, Na Bukatar Naira Biliyan 189


Jami'an hukumar zaben Nigeria, INEC, a gaban kwamitocin kasafin kudi na majalisun tarayyar Nigeria

Hukumar zaben Nigeria, INEC, a karkashin jagorancin Farfesa Mahmud Yakubu, ta gana da kwamitocin kula da harkar zabe na majalisar dokokin Nigeria domin bayyana bukatun hukumar game da zaben shekarar 2019

Shugaban hukumar zabe ko INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya jagoranci jami’ansa a gaban kwamitocin kula da harkar zabe na majalisar dattawan dana wakilai domin yin bayani dangane da kudin da suke nema na gudanar da zaben shekarar 2019.

Farfesa Mahmud Yakubu yace suna bukatar kudi kimanin Naira biliyan 189 ne da za su kasa gida hudu. A ciki za’a biya ma’aikata zabe da kwamgilar buga takardun zabe da bangaren gudanar da ayyukan zabe, sai kuma kudin da za’a ware domin bukatu na musamman.

Kwamitocin kasafin kudi na majalisun Nigeria sun gana da jami'an INEC
Kwamitocin kasafin kudi na majalisun Nigeria sun gana da jami'an INEC

Shugaban hukumar zaben y ace idan an yi la’akari da zaben shekarar 2015, Naira biliyan 120 ne kawai aka kashe. Amma yanzu hukumar na neman Naira biliyan 189, an samu karin Naira biliyan 69. Yace dalilin banbancin shi ne karin masu jefa kuri’a da aka samu. A shekarar 2015 mutane miliyan 70 ne aka yiwa rajista. Amma a wannan shekarar an samu karin mutane miliyan 12 da ‘yan kai. Idan aka kwatanta da na shekarar 2015 an samu mutane miliyan 82 da za su kada kuri’a a zaben 2019.

Sanata Suleiman Nazir shugaban kwamitin harkar zabe na majalisar dattawa yace zaman kwamiti daban yake. Idan sun gama abun da su keyi sai su kai gaban majalisun, ayi muhawara a kai.

Dangane da naurar nan mai tantance masu zabe, da ake cewa card reader da turance, Sanata Suleiman Nazir y ace naurar ce ta basu nasara a zaben 2015, saboda haka suka yi doka cewa ba za’a yi zabe a kasar ba sai da naurar. Naurar ta na hana yin magudi.

A saurari rahoton Medina Dauda

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG