Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ingila Ta Bayyana Damuwa 'Yan kasarta Suna Shiga Aikin Ta'addanci A Somaliya


Al-Shabaab, Somalia.

Ministan aiyukkan raya kasashen ketare na Ingila ya bayyana damuwa da ganin yadda ake ta samun ‘yan asalin Ingila din suna tafiya Somalia, suna yaki tareda kungiyoyin da Ingila din ke cewa na ‘yan ta’adda ne

Ministan aiyukkan raya kasashen ketare na Ingila ya bayyana damuwa da ganin yadda ake ta samun ‘yan asalin Ingila suna tafiya Somalia, suna yaki tareda kungiyoyin da Ingila ke cewa na ‘yan ta’adda ne.

A yau ne minister Andrew Mitchell yake cewa a zaman da ake a yau, ba wata kasa a duniyar nan dake da ‘yan kasa masu yawa dake a sansanonin ‘yan ta’addar Somalia kamar ‘yan Ingila.

Ministan yace Biritaniya ta kudurta karfafa rawar da take takawa a Somalia saboda tinkarar barazanar da ke fito mata daga can Somaliya.

A cikin shekara mai zuwa ake shirin wani babban taron kasa-da-kasa a London akan wannan tashin hankalin na Somaliya inda shugabannin kasashe zasu duba barazanar da kungiyar al-Shebab ke yiwa duniya da kuma bukatun mutanen Somaliya dake jin jiki a sanadin Farin da ya abkawa kasar.

Aika Sharhinka

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG