Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi a Iraki sun ce wani bam da aka dana a mota a wani wurin jana’iza dake birnin Bagadaza ya kashe mutane 37


Mutane suna kallon motar da ta tarwatse a wurin da aka kai harin bom kan wata runfar da ake jana'iza a yankin 'yan Shi'a dake Bagadaza, Iraq.

Bom da aka dana a wajen wata jana'iza a birnin Bagadaza ya kashe mutane 37

Hukumomi a Iraki sun ce wani bam da aka dana a mota ya tashi a wani wurin jana’iza a birnin Bagadaza, ya hallaka akalla mutane talatin da bakwai.Bom din da ya tarwatse yau Alhamis a yankin ‘yan Shi’a ya kuma raunata mutane a kalla mutane saba'in da takwas. A kuma unguwar Karradah ta birnin na Bagadaza, wani bam din da aka dana a gefen hanya ya kashe mutum guda ya kuma raunata a kalla mutane biyar. Uku daga cikin wadanda suka sami raunukan ‘yan sanda ne. Wani bam din da aka dana a gefen hanya har ila yau kuma, a yankin Bab al-Maudham, ya kashe mutum guda ya raunata wasu uku. An sami karin tashe-tashen hankula a Iraki a ‘yan kwanakin nan, a inda ake ta auna bama bamai kan ‘yan Shi’a da kuma jami’an tsaro.

XS
SM
MD
LG