Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Agadez Sun Cafke Mutane 17 da Suka Hada da 'Yan Najeriya


 Mohamed Bazoum ministan tsaron cikin gidan Nijar
Mohamed Bazoum ministan tsaron cikin gidan Nijar

Jami'an tsaron jihar Agadez a Jamhuriyar Nijar sun cafke mutane goma sha bakwai, mace daya, maza goma sha shida kuma biyu daga cikinsu 'yan tarayyar Najeriya ne.

Cafke mutanen ya biyo bayan wani samame ne da jami'an tsaro suka kai cikin garin Agadez da kewayensa a wani matakin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsanaki a jihar ta Agadez.

Mutanen da aka cafke ana zarginsu ne da safaran miyagun kwayoyi da suka hada da koken da tamol da dai sauransu. Wasu kuma cikinsu ana zarginsu da mallakar miyagun makamai da suke anfani dasu wajen yin fashi a hanyoyi da afkawa jama'a tare da kwace dukiyoyinsu

Abis Idrisa Muhammad mataimakin mai shigar da kara a jihar Agadez yace mutane ne da sun yi Allah wadai da dokokin kasa suna aikin asha. Yace suna sayar da kwayoyi. Suna sayarda bindigogi kana su amshewa mutane kayansu. Suna kwacewa mutane motoci

Kwayar wiwi da suke sayarwa daga kasashen dake makwaftaka da Nijar suke samota.

Sama da bindigogi goma ne aka kama a samamen.

Wakilin gwamnan jihar Agadez Sadu Saloke ya kira al'umma da su bada hadin kai wa jami'an tsaro domin cimma nasarar ayyukansu. Ya kira mutane su dinga bada labari idan sun ga mutane suna shigowa.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

XS
SM
MD
LG