Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Amurka Sun Amince Da Sabon Maganin Ciwon Suga Na Kamfanin Johnson & Johnson


Ana gwajin jinin wani mai ciwon suga
Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta Amurka da ake kira FDA a takaice ta amince da wani sabon maganin ciwon suga da kamfanin Jonson & Johnson ya sarrafa, ya kuma kasance irinshi na farko da Amurka ta amince da shi.

Hukumar ta amince da amfani da maganin da ake kira Invokana bayan bincike ya nuna cewa, yana rage karfin suga dake cikin jinin mutanen da suke da ciwon suga nau’in da ake kira “type 2” wanda yawancin masu ciwon suga suke fama da shi.

Hukumar FDA ta amince da amfani da maganin ne bayan gwajin maganin a matakai biyar domin tabbatar da ingancinhi.

Maganin yana rage karfin suga dake jinin mutum ta wajen tsotse sinadarin dake sa suga ta wuce kima ya kuma sa mutum ya rika yawan fitsari.

Ciwon suga yana kashe kwayoyin halittar da suke karawa mutum karfin jiki da ake kira gulukos r ta wajen age yawan gulokos din dake shiga cikin hanyar jinin mutum ya rika fice ta fitsari abinda ke haifar da ciwon suga. Idan mai ciwon suga mai sami jinya yadda ya kamata ba, yana iya lalata kodarsa ko kuma ya makance.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG