Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Jamus Sun Tsare Mutane Shida Da Ake Zargin Suna Shirin Kai Hari


Shugabar Kasar Jamus Angela Merkel

Sakamakon bayanan sirri da ofishin lauyoyi ya bayyanawa 'yan sandan Berlin an cafke mutane shidan dake shirin kai hari akan 'yan kallo da masu wasan guje-guje a birnin Berlin

Hukumomin Jamus sun ce an tsare mutane shida a jiya Lahadi da ake zarginsu da hannu a cikin harin da yan ta’adda ke shirya kaiwa wani shirin wasan guje guj a birnin Berlin.


A wata sanarwar hadin gwiwa, lauyoyi da yan sanda sun ce, akwai alamomi na musamman dake nuna wadanda aka kama masu shekaru daga 18 zuwa 21, suna cikin masu shirya wannan danyen aikin a kan wasan guje gujen


Yan sandan Berlin sun dora a shafinsu na twitter cewa sun kama mutane shida biyo bayan wani aikin hadin kai tsakanin yan sandan Berlin da ofishin lauyoyin kara.


Wata jaridar Jamus ta Die Welt ce ta fara bada labarin yan sanda sun yi nasarar dakile shirin wani hari a kan masu kallon wasan guje guje da ma masu wasan da wukake.

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Hira da Yusuf, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar da ya shekara a Abuja yana sana’r gyaran takalmi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
XS
SM
MD
LG