Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Nijar Sun Gano Gawarwakin Mutane 34


Irin bakin hauren dake shiga Nijar suna bin ta hamada domin zuwa Turai cikin yanayin mugun zafi da rashin ruwan sha.
Irin bakin hauren dake shiga Nijar suna bin ta hamada domin zuwa Turai cikin yanayin mugun zafi da rashin ruwan sha.

Tun ba yau ba shugaban kasar Nijar yace mutane daga wasu kasashen Afirka sun mayar da kasarsa wata zangon ratsawa ta zuwa nahiyar Turai lamarin da kan sa wasunsu su rasa rayukansu ko a cikin hamada ko kuma cikin tekun baharum

A Nijar, hukumomin kasar sun ce sun gano gawarwakin mutane 34, inda 20 daga cikinsu yara ne da suna kokarin ketare hamada.Jami'an gwamnati suka ce sun hakikance mutanen 'yan ci rani ne da suka doshi arewa da fatan su kai Aljeriya, ko kuma Turai.

Ma'aikatar cikin gidan kasar ce ta bada wannan sanarwar gano gawarwakin jiya Laraba. A cikin bayanin da aka yi a tashar talabijin tace mata tara da maza biyar da yara 20 din sun mutu ne sakamakon kishin ruwa,bayan da masu safarar mutane suka yi watsi da su a hamada.

Har yanzu ba'a tantance ko mutanen 'yan wace kasa ba ne. Kungiyar kula da 'yan gudun hijira ko ci rani ta kasa da aksa tace adadin masu irin wannan tafiye tafiyen ya karu sosai daga yankunan da suke kudu da hamadar sahara zuwa Turai, musamman daga kasashe da suke yamma da kuma Afirka ta Tsakiya.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG