Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Pakistan Sun Ba 'Yan Gudun Hijira Kwana Uku Su Yi Rajista


'Yan gudun hijira daga Afghanistan dake Pakistan
'Yan gudun hijira daga Afghanistan dake Pakistan

Hukumomi a Pakistan sun ba dubban iyalan da suka yi gudun hijira zuwa Afghanistan shekaru 2 da suka wuce a kokarin gujewa rikicin ‘yan bindiga daga nan zuwa litinin, su je su yi rijista don komawa kasarsu.

Hukumomin na Pakistan sun yi ta kokarin su ga iyalan dake arewacin yankin Waziristan sun koma kasarsu watannin da suka wuce, amma ranar Laraba jami’ai sun fidda wata sanarwa a hukumance ta cewa an basu daga nan zuwa 1 ga watan Agusta su bada takardun istarsu, abinda hukumomin suka ce sun riga su rarraba ga iyalan da ke gudun hijira ta hanyar shugabannin al’ummominsu. Wadanda kuma basu yi ba, ka iya fuskantar matsalolin wajen komawa gida.

A cewar hukumar da ke sa ido akan hakkokin bil’adama ta MDD, daga watan Disambar shekarar 2014, mutane fiye da dubu dari biyu da cisi’in da daya da dari takwas suka tsallake zuwa aghanistan. Yawancinsu sun sauka a sansanin Gulan a Gurboz dake gundumar Khost. A watan Mayu n shekarar da ta gabata, Khost da Paktika sun sauke iyalai 32,576, kusan mutane 205,000 ke nan.

XS
SM
MD
LG