Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Tashi A Kauyen Idlib Ya Kuma Kashe Fararen Hula


Wajen da bam din ya tashi

A kalla fararen hula 23 ne suka mutu a wani harin bam din mota da aka kai a birnin Idlib dake Syria

Babu kungiyar da ta dauki alhakin wannan hari. A cewar kungiyar duba da kare hakkin bil’adama an kai harin ne kan babban ofishin wata kungiyar ‘yan tawaye .

Birnin da lardin na karkashin ikon ‘yan tawaye da ‘yan bindiga da dama masu kokarin mamaye yankin, cikin su kungiyar data fi kowacce karfi, itace wata mai alaka da Al-qaeeda.

Kungiyar duba hakkin bil’adama ta Syria tace dakarun shugaban kasar Bashar Assad, sun kwato kauyuka kusan 60 da kuma kauyuka dake kan iyaka tsakanin Idlib da makwaftan ta a yankin Hama, tun soma aikin sojoji a watan Oktobar da ta gabata.

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG