Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Cikin Mawuyacin Hali - In Ji Mutumin Da Likita Ya Cire wa Koda


Isa Hamman Mutumin Da Likita Ya Cire wa Koda

Wani mutum a Yola da ke jihar Adamawa a arwea maso gabashin Najeriya, ya tsinci kansa a wani mawuyacin hali, bayan da wani likita ya cire mai kodoinsa yayin da ya je da kuken ya na fama da ciwon ciki.

Bayan an yi masa gwaje gwaje ne aka umarci Isa Hamman da ya kawo dubu 50 a yi masa aiki,wato tiyata, kuma bai yi kasa a gwiwa ba ya biya,inda likita ya yi masa aiki.

To amma abun takaici da ban tausayi sai aka cire masa dukkanin kododinsa,wato kidney,batun da yanzu ya jefa shi cikin mawuyacin hali.

‘’Ni ban san abun da suka yi ba, sai bayan da abu ya baci har muka je Gombe,don Allah ku taimaka min.’’

Domin jin yadda aka kare da kuma matakin da ake shirin dauka, saurari rahoton wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz daga Yola:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG