Wani babban jami’in kasar India mai ba da shawara a fannin tsaro, ya zargi wani gungun tsageru da kokarin kutsa kai cikin yankin Kashmir, yana mai cewa Pakistan na yunkurin ta-da zaune-tsaye.
Mai bai wa firai ministan India Narendra Modi shawara kan harkokin tsaron kasa, Ajit Doval, ya fadawa manema labarai cewa, wasu ‘yan ta’adda 230 suna shirin kutsa kai zuwa sassan yankin na Kashmir.
Doval ya kara da cewa, ana kuma fasakorin makamai zuwa cikin yankin, sannan an umurci jama’ar da ke Kashmir da su ta da rikici.
Dakarun India sun ce, sun samu wadannan bayanai ne daga kutsen da suka yi a sakonnin rediyo da kuma bayanan sirrin da aka tattara.
Ita dai India ta sha zargin Pakistan da mara baya tare da horar da mayakan sa-kai da nufin su ta da boren neman ballewa, zargin da hukumomin Islamabad suka sha musantawa.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 31, 2023
Fafaroma Francis Ya Kai Sakon Zaman Lafiya A Afirka Ta Tsakiya
-
Janairu 30, 2023
Mutane 88 Sun Mutu A Wani Harin Bomb A Pakistan
-
Janairu 18, 2023
Mataimakin Shugaban Gambia, Badara Alieu Joof Ya Rasu A India