Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

India Ta Kaddamar Da Shirin Bada Riga Kafin COVID-19


Bada riga kafin cutar COVID-19 a India.
Bada riga kafin cutar COVID-19 a India.

Yayin da India ta kaddamar da shirin bada riga kafin a kasar adadin mace-mace a kasashen duniya ya zarta miliyan biyu.

Ranar Asabar 16 ga watan Janairu kasar India ta fara gagarumin shirinta ta na bada riga kafin cutar COVID-19. Masu muhimman ayyuka kamar jami’an lafiya su ne aka shirya zasu fara karbar riga kafin.

An kaddamar da shirin ne bayan da Firai Minista Nerandra Modi ya gabatar da wani jawabi ga 'yan kasar ta talabijin.

Mace-mace sakamakon cutar COVID-19 da aka samu a fadin duniya sun zarta miliyan biyu a jiya Juma’a, a cewar jami’ar Johns Hopkins, shekara daya bayan da aka gano cutar a birnin Wuhan da ke China.

Sakatare Janar din Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya fada wa manema labarai a jiya Juma’a cewa adadin mace-macen ya yi muni ne saboda rashin hadin kan kasashen duniya a kokarin yaki da cutar, ya kara da cewa bangaren kimiyya ya yi nasara amma hadin kai ya gaza.

XS
SM
MD
LG