Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyara ofishin hafsan sojin saman Najeriya IO Amao a Abuja babban birnin kasar.
Shugaban hukumar zaben ya nemi taimakon rundunar sojan saman Najeriya wajen ganin an isar da kayan zaɓe a ƙananan hukumomi a lokaci guda lokacin zabe.
Yakubu yace aiki da rundunar shine mafita wajen kare yiwuwar samun tsaiko wajen isar da kayayyakin zabe musamman a yayin da hukumar ke kokarin ganin tayi zaben gwamna a jihar Ekiti akalla nan da makwanni biyu masu zuwa.
Ya jaddada muhimmancin kai kayayyakin zabe a runfunan zabe 190,000 lokacin zaben 'yan majalisu a duk fadin kasar, wanda ake bukatar ganin anyi zabe a lokaci guda wato daga karfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na yamma.
Yayin jawabinsa hafsan sojin saman Nijeriya, Amao yace rundunar a shirye take don ganin ta taimakawa hukumar ta INEC wajen gudanar da ayyukan zabe ba tare da wata matsala ba.
Dubi ra’ayoyi
Ko ka yi rijista da mu? Shiga shafinka
Ba ka yi rijista da mu ba? Yi rijista
Load more comments