Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC Za Ta Fito Da Sabbin Hanyoyin Bayyana Sakamakon Zabe


Shugaban Hukumar Zaben Najeriya, INEC, Farfesa Mahmud Yakubu
Shugaban Hukumar Zaben Najeriya, INEC, Farfesa Mahmud Yakubu

Hukumar Zaben Najeriya, INEC ta ce duk da shirin yin anfani da naura mai kwakwalwa wajen sanar da sakamakon zabe daga rumfunan zaben, hakan bai hana cike takardu ba da sakamkon zaben.

Sabon matakin da hukumar zaben Najeriya, INEC, ta dauka na sanar da sakamakon zabe da na'ura mai kwakwalwa ko ta tauraron dan Adam tun daga rumfar zabe ba zai hana cika sakamakon kan takarda kamar yadda aka saba ba.

Jami'in yada labaran hukumar, Aliyu Bello, ya ce yin amfani da na'urar wani karin inganci ne akan abun da aka yi a baya.

Ya kuma ce za'a tabbatar da wadatattun batura ko na'urorin wuta domin kaucewa samun cikas a fannin wutar lantarki.

A cewar Aliyu Bello hukumar ta ga ya dace a yi amfani da kafofin zamani domin jami'in zabe ya aika da sakamakon daga rumfunar zabe kafin ma ya kai takardunsa.

Sai dai tuni masana a harkar zabe suka fara bayyana ra'ayinsu kan wannan sabon mataki.

Saurari abin da Alhaji Musa Muhammad Gidado Garba Gana, wani mai fashin baki ya ce dangane da wannan sabon tsari a wannan rahoto da wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG