Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Tayi Barazanar Kai wa Sojojin Amurka dake Gabas Ta Tsakiya Hari Idan Ta Kakaba Mata Takunkumi


Janar Mohammad Ali Jafari kwamandan rundunar sojojin juyin juya halin kasar Iran

Janyewar Amurka daga yarjejeniyar shirin nukiliyar Iran kamar yadda take cewa zata yi zai ba majalisar dattawan Amurka damar kakaba wa Iran sabbin takunkum lamarin da ya sa kasar Iran din ta sha alwashin maida martani da harin makami mai linzami kan sojojin Amurka dake Gabas Ta Tsakiya

Kwamandan Askarawan Tsaro na Musamman na juyin juya halin Iran, ya yi gargadi ga sansanonin sojin Amurka da ke yankin Gabas Ta Tsakiya cewa za su fuskanci yiwuwar harin makami mai linzami daga Iran muddun Amurka ta kakaba wa Iran sabontakunkumi.

Shugaban Amurka Donald Trump na shirin yin shela cikin 'yan kwanaki masu zuwa cewa Iran ba ta kiyaye yarjajjeniyar kasa da kasar da aka cimma a 2015 na dakile shirin makamin nukiliyarta, to amma zai baiwa Majalisar Dokokin Amurka din wa'adin kwanaki 60 don yanke shawarar ko a kakaba ma Iran sabbin takunkumi ko a'a.

Sai dai kuma kafafen yada labaran Iran sun ruwaito Kwamandan Askarawan Tsaron kasar, Mohammad Ali Jafari na gargadi jiya Lahadi cewa muddun aka kakaba masu sabbin takunkumi, to sai dai ko Amurka ta kawar da sansanonin sojinta zuwa da'irin nisan kilomita 2,000 da makamai masu linzami na Iran ke iya kaiwa.

Sansanonin sojin Amurka din na kasashen Bahrain da Iraq da Oman da Afghanistan ne, wadanda dukkansu ba su wuje nisan kilomita 500 daga kan iyakar Iran ba.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG