Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

IRAQ: Jirgin Yakin Ya Jefa Bom a Baghdad Ya Kashe Mutane da Rushe Gidaje


Wurin da wani jirgin yaki ya jefa bam cikin kuskure
Wurin da wani jirgin yaki ya jefa bam cikin kuskure

A yau Litinin ne wani jirgin yakin kasar Iraqi ya jefa bom a kan wata unguwa dake gabashin Baghdad, ya kashe a kalla mutane 7 amma sojojin kasar sun bayyana lamarin a matsayin hatsari.

Mai magana da yawun sojojin yace jirgin yakin Sukhoi kirar Rasha, ya sami matsalar injin ne, abinda yassa ya sako bom yayinda yake kokarin komawa mazauninsa dake wani sansanin soja.

Sakamakon faduwar bom ‘din ya lalata gidaje masu dinbin yawa da raunata a kalla mutane 11.

Anyi amfani da jirgin yakin ne a hare haren da ake kaiwa kan kungiyar IS, wanda suka kame wasu manyan bangarori a Arewa da yammacin Iraqi a shekarar da ta gabata.

Sojojin Iraqi na daga cikin kungiyar kawance da Amurka ke jagoranta wajen kai hare hare ta sama, haka kuma suna aika sojojin su domin taimakawa mayakan tsageru dake fafatawa wajen ganin sun kwato yankunan su dake hannun mayakan sakai.

Mayaka masu goyon bayan gwamnati na samun nasara, amma mayakan sa kai na rike da yankunan da suka kwace masu yawa, ciki harda wasu mayan birane.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG