Accessibility links

Iraqi Ta Soke Yarjejeniyar Sayan Makamai Data Kulla Da Rasha.


Frayin ministan Rasha Dmitry Medvedev yake gaisawa da PM Nouri Al-Maliki,na Iraqi.
Tana kasa tana dabo kan yarjejeniyar cinikin makamai tsakanin Rasha da Iraqi na zunzurutun kudi dala milyan dubu hudu da metan.

Kakakin PM Iraqi Nouri al-Maliki, ya fada jiya Asabar cewa an soke cinikin, sabo da gwamnatin kasar tana shakkar an saka rashin gaskiya cikin yarjejeniyar. Amma wasu jami’an kasar suka ce ana dai sake nazarin shirin baki dayansa.

A cikin watan jiya ne Bagadaza da Moscow suka sanya hanu kan yarjejeniyar.
Rahotanni sun ce da za a sa jiragen yaki masu saukar angulu samfirin Mi-28 guda 30 cikin yarjejeniyar cinikin, idan har hakan ya kasance, Rasha zata zama ta biyu wajen samarwa Iraqi kayan yaki, bayan Amurka.

Kamfanin dillancin makamai na Rasha yaki yace uffan kan wannan batu. Sai dai babu karin bayani ko Iraqi tana auna zargin cin hanci da rashawa kan Moscow ne ko kuma akan jami’an gwamnatin kasarta.
XS
SM
MD
LG