Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isira'ila Ta Dakatar Da Shirin Korar 'Yan Afirka Bakin Haure


Israeli Prime Minister Benjamin

A wani al'amari na ba-zata, kasar Isira'ila ta dakatar da shirinta na tasa keyar bakin haure 'yan Afirka zuwa kasashensu. To amma murna na iya komawa ciki ga bakin, muddun 'yan Majalisar Dokokin kasar su ka kafa dokar korar.

Gwamnatin Isira’ila ta dakatar da shirinta na tasa keyar dubban baki ‘yan Afirka, wadanda su ka shiga kasar bisa ka’ida ba, bayan da yinkurinta na baya-bayan na mayar da su Afirka ya ci tura. Tuni bakin hauren, wadanda akasari su ka fito daga kasashen Eritrea da Sudan su ka shigo Isira'ila daga ta kasar Masar, ke ta murna.

A kalla yanzu kam, ‘yan Afirka, wadanda wasunsu sun zauna a Isira’ila na tsawon shekaru 10, za su iya sabunta takardun izinin zamansu duk bayan kwanaki 60. Tun daga 2013, wani bangare na bakin hauren ya amince da wani shiri na tura su kasashen Rwanda da Uganda. Da yawansu na cewa guje ma yaki da take hakkin dan adam su ka yi.

Firaministan Isira’ila Benjamin Netanyahu, wanda ke fuskantar matsin lamba a siyasance kan cewa ya yi wani abu, ya rubuta a kafar twitter cewa ya na da niyyar sake bude wani wurin tara bakin hauren wanda ke can lungu, a yayin da kuma ‘yan Majalisar Dokokin kasar ke iya sake kafa wata doka ta fitar da bakin hauren.

Kafin nan ma, Mr. Netanyahu ya soke wata yarjejjeniyar da su ka cimma da hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Majalisar Dinkin Duniya ta tura rabin bakin hauren zuwa Yammacin duniya a bar sauran kuma su zauna a Isira’ila din.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG