Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Duniya

Iskar "Isaias" Na Iya Zama Guguwa - Kwararru


Yadda Iskar Isaias ta sauya yanayi jihar Florida

Masu hasashen yanayi sun yi gargadin cewa iskar Isaias wacce aka yi gargadin cewa za ta tunkari jihohin North da South Carolina za ta Iya zama karamar guguwa.

Tun a jiya ne aka yi gargadi kan yiwuwar saukar ruwan saman kamar da bakin kwarya hade da iska mai karfin gaske a jihohin.

Ana sa ran saukar ruwan saman ne a daren yau Litinin a yankin da ke kan iyakar jihohin North da South Carolina.

Cibiyar da ke sa ido kan aukuwar bala’in guguwa ta ce, iskar ta Isaias za ta ci gaba da tafiya akan doron kasa yayin da za ta ratsa ta jihar Georgia ta kuma nufi jihohin na Carolinas.

Yadda iskar Isaias ke sanya wani teku kadawa
Yadda iskar Isaias ke sanya wani teku kadawa

Kiyasin da aka yi da safiyar yau Litinin ya nuna cewa Isaias na tafiyar kilomita 110 cikin sa’a guda, sannan za ta kara karfi ta koma guguwa a lokacin da za ta sauka.

Yankunan da aka yi wa gargadin su zauna cikin shirin kar-ta-kwana, sun hada har da yankin Long Island da ke New York.

Tuni dai aka saka dokar ta baci a jihohin na North da South Carolina domin lamarin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG