Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Kaiwa Sojojin Syria Hari Ta Sama


Wani farmaki ta sama da Isra’ila ta kai a kan tungar sojin Syria ya kashe soja daya kana ya raunata wasu biyu, ya kuma lalata wani ma’ajiyin makamai, a cewar ma’aikatar labaran kasar Syria.

Harin da aka kai kan tungar ta T4, a tsakiyar lardin Homs na zuwa ne sa’o’I bayan da Isra’ilan ta kai wani farmaki a Golan Height dake kudancin Syria.

Isra’ila bata yi wani bayani game da harin a kan tungar sojojin ba, amma dai tace harin da ta kai a Golan martani ne ga rokar da aka harbor mata a ranar Asabar daga Syria.

Firai ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fada a jiya Lahadi cewa ba zasu lamunta da duk wani makami da za a harba zuwa cikin kasarsu ba.

Cibiyar kare hakkin bil adama ta Syrian Observatory tace farmakin Isra’ila a kan Golan Heights ya kashe mutane goma cikin har da sojojin Syria da ma mayakan kasashen waje.

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Zauren VOA daga jihar Kaduna Alan Almajiranci da Cin Zarafin Mata - 3

Zauren VOA daga jihar Kaduna Alan Almajiranci da Cin Zarafin Mata - 3-1
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:55 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
XS
SM
MD
LG