Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Harbo Jirgin Yakin Siriya


Mayakan sojin Kasar Isra'ila sun ce sun harbo wani jirgin yakin Siriya yau talata bayan ya shiga sararin samaniyar Isra'ila.

A wata sanarwa da mayakan kasar Isra'ilan suka fitar, sun ce sun harbo jirgin da makamai masu linzami bayan ya shigar masu yankin kasa.
Gidan radiyon sojojin Isra'ila yace sun harbo jirgin ne a filin da suka mamaye na Golan Heights amman kila ya fadi ne a yankin da suke iko dashi na Siriyan.
Gidan radion ya kara da cewa basu san wane hali matukin jirgin yake ciki ba.
Gidajen watsa labaran Kasar Syria sun ce an harbor masu jirgi ne a lokacin da yake kokarin kai hari a sararin samaniyar Syria.
Isra'ila ta kwace Golan Heights daga Siriya a shekarar alif dari tara da sittin da bakwai. Majalisar dinkin duniya ta aika da mayakan zaman lafiya bayan shekara 2.

Facebook Forum

Ramaphosa Ya Kai Ziyara Najeriya

Lokacinda Ramaphosa Ya Isa Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG