Accessibility links

Isra'ila Ta Kai Hare-Hare A Zirin Gaza


Wata mace tana wucewa gaban wani gida da Isra'ila ta rusa a wani sumame da ta kai a Zirin Gaza.
Jiragen saman yakin Isra’ila sun kai hare-hare kan wuraren da ake zargin Falasdinawa na amfani dasu a Zirin Gaza, wajen harba rokoki zuwa kan Isra’ila.

Mayakan Falasdinawa biyar sun halaka, cikinsu harda wanda ake zargin shine jagoran kungiyar SALAFAWA mai dangantaka da al-Qaida.

Jami’an ayyukan Agaji a Zirin Gaza suka ce harin farko na jiragen saman yakin Isra’ila sun kashe mayakan Falasdinu biyu da shi kansa kwamandan mayakan Salafawa a Arewacin Gaza; a hari na biyu kuma an kashe dan jihadin Falasdinu guda da jikkata wasu falasdinawn dake kan Babura a kudancin Zirin Gaza jiya lahadi da safe, amma hari na uku shine yafi jikkata Mayakan Falasdinawa.
XS
SM
MD
LG