Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISRAILA: Yahudawan Habasha Sun Fusata


'Yansandan Israila sun yi arangama da Yahudawan Habasha masu zanga-zanga
'Yansandan Israila sun yi arangama da Yahudawan Habasha masu zanga-zanga

Biyo bayan dukan wani soja dan asalin Habasha da 'yansandan Israila suka yi tarzoma ta barke a kasar

Shugaban kasar Israila Reuven Rivilin ya fada jiya Litinin cewa zanga-zangar da Yahudawa ‘yan asalin Habasha keyi saboda da nuna masu wariyar jinsi da musgunawar da ‘yansanda suke yi masu tamkar allura ce ta tono garma kuma yakamata kasar ta shawo kan matsalar.

Yayi jawabin ne bayan da dubun dubatan mutane suka yi maci zuwa cikin taskiyar Tel Aviv lamarin da ya jawo rufe manyan tituna inda suka kara da ‘yansanda.

Bamu lura ba kuma bamu saurari korafe-korafen mutane ba, inji Mr. Rivlin. Yace mu ba bakin juna ba ne. Mu ‘yanuwan juna ne saboda haka kada mu kuskura mu gina kasar da zamu yi nadama akanta wata rana.

Jiya Litinin an kara yin zang-zanga a Birnin Kudus yayin da Firayim Ministan kasar Benjamin Netanyahu ke kokarin ganawa ‘yan asalin Habashan.

Takaddama ta taso ne bayan da wani faifan bidiyo ya nuna yadda wani dansanda ke lakadawa wani dan asalin Habasha cikin kayansa na soji.

Yanzu dai a kasar Israila akwai yahudawa ‘yan asalin Habasha 135,000.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG