Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iyalan Fasinjan Jirgin Kasa Da Aka Sace Sun Musanta Jita-Jitar Sakin Fasinjojin


Cikin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna.
Cikin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna.

Kungiyar 'yan'uwan wadanda aka sace a jirgin kasar da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja sun sanar da duniya cewa labarin sakin su labari ne na kanzon kurege amma akwai hasken nasara game da yuwuwar sakin mutanen nan bada dadewa ba.

A Laraban nan ne dai labarin sakin mutanen da 'yan-bindiga su ka kama su ka dunga yawo a kafafen sada zumunta har ma wasu na cewa duk mutanen da aka kama sun koma gida, sai dai daya daga cikin 'yan'uwan wadanda aka sacen ya ce labarin ba shi da tushen gaskiya.

Wannan dai ba shine karo na farko da labarun kanzon kurege ke yawa game da sakin mutanen da 'yan-bindiga su ka kama ba, abun da ya sa masani kan harkokin tsaro, Manjo Yahaya Shinko mai ritaya ya ce salo ne na saka siyasa aka fito da shi.

Mai magana da yawun hukumar jiragen kasan Najeriya malam Mahmud Yakubu ya shedawa Muryar Amurka cewa, ba su san komai game da sakin wadanda aka kama ba sai dai shi Malam Sani Lawal din da 'yan-uwan shi biyu ke hannun 'yan-bindigan ya ce kwanaki saba'in da biyu (72) da kama 'yan'uwan su, suna cikin wani hali.

Har yanzu dai babu wani labari game da cigaba da aikin jirgin kasan Abuja-Kaduna tun bayan yunkurin cigaba da aikin da ya yi karo da zanga-zangar 'yan-uwan wadanda aka sace a Kaduna.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG