Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jagoran Addini A Iran Ayatollah Ali Ya Caccaki Saudiyya


Ayatollah Ali Khamenei

Jagoran addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya nanata shakkarsa akan ko Saudiya zata iya tattalin wurare masu tsarki na Musulunci, kuma ya zargi masarautar kasar da kashe mahajjata a wani turmutsutsu da ya faru a hajin bara.

Khamenei yace yan Saudia marasa tausayi masu kashe bayin Allah sun hada wadanda suka mutu da masu rauni a wuri daya a maimakon a basu magani ayi musu jinya ko kila za’a cetosu. Yace su suka kashesu. Khamenei yayi wa’yanna kalaman ne a wata sanarwa da ya dora akan shafinsa na yanar gizo, na cika shekara daya da faruwar wannan bala’i. Sai dai bai bada wata shaida ba akan zargin da yayi.

Nan take Saudiya ta mayar mai da martini, inda Yarima mai kula da harkokin cikin gida Mohammed bin Nayef, yace Iran tana kokarin sa siyasa acikin harkar haji da ake bukatar akalla kowane musulmi ya samu a cikin rayuwarsa.

A cewar gwamnatin Sadia turmutsumutsun na bara yayi sanadiyar mutuwar mutane 769, to amma kampanin dillacin Labarai na AP tace yawan mutanen da suka rasa rayukkansu a cikin hargitsin sun kai mutane dubu biyu da dari hudu da 26 bayan ta tattara jawaban da wasu kafofin yada labarai na cikin da jami’ai da yan kasashensu suka je haji.

Ita kuwa gwamnatin Iran tace mutane 464 da suka mutu duk Iraniyawa ne kuma sun dora laifin wannan bala’i a kan gazawar gwamnatin Saudia.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG