Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jagoran Dakarun Da Suka yi Juyin Mulki a Sudan Ya Yi Murabus

Jagoran dakarun kasar Sudan, Janar Awad Mohammad Ahmed Ibn Auf (hannun hagu a tsaye)
Jagoran dakarun kasar Sudan, Janar Awad Mohammad Ahmed Ibn Auf (hannun hagu a tsaye)

Manjo- Janar Awad Mohammad Ahmed Ibn Auf, ya nada Janar Abdel-Fatah Burhan a matsayin magajinsa.

Jagoran dakarun kasar Sudan da suka hambare gwamnatin shugaba Omar Al Bashir, ya sauka daga mukaminsa, kwana guda bayan da sojoji suka sanar da cewa sun karbe ikon mulkin kasar.

Manjo- Janar Awad Mohammad Ahmed Ibn Auf, ya nada Janar Abdel-Fatah Burhan a matsayin magajinsa.

Dakarun kasar dai ba su fadi dalilin da ya sa Auf ya sauka ba.

A jiya Juma’a jama’a sun ci gaba da zanga zanga a Khartoum, babban birnin na Sudan, inda suke adawa da matakin da wata majalisar sojin kasar ta dauka na daukar ragamar tafiyar da gwamantin wucin har na tsawon shekaru biyu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG