Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yabawa Jahar Nija Kan Kokarin Wadata Jama'a Da Ruwa Da Kare Muhalli.


Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello

Shugabar wata kungiya wacce ta sanya hanu kan yarjejeniyar fahimtar juna da jahar Parfessa Patricia ce tayi wannan yabo a New York.

Wata kungiya mai zaman kanta wacce ta shahara wajen kididdiga da tara bayanai gameda kasa da al’umma, ta yabawa jahar Nija dake arewacin Najeriya, saboda kasancewarta kan gaba wajen tanadin ruwa da kare muhalli.

Parfessa Patricia McCain, shugabar wata kungiya mai zaman kanta da ake kira World Council on City Data, ko WCCD a takaice ce tayi wannan yabo, lokacinda take sanya hannu a madadin kungiyar da gwamnatin jahar Naija, domin samarda bayanai da zasu taimaka wajen ayyukan ci gaba a jahar.

An yi bikin sanya hanun ne a ofishin jakadancin Najeriya dake birnin New York.

Parfessar ta yabawa jahar wajen karfafawa mata guiwa su yi takara, da kuma jahar tana hobbasawa wajen dashen itatuwa.

Da yake amsa tambaya gameda halin tsaro a jahar da zai karfafa masu zuba jari guiwa so je jahar Nija, Gwamna Abubakar Sani Bello, yace ai wannan shine mataki na farko da kungyar ta WCCD ta yabawa jahar akai.

Gameda tsarabar da zai kaiwa al’ummar jaharsa bayan wannan ziyara, Gwamna Sani Bello, yace jahar tana kokarin kulla wata yarjejeniya da jahar Pennsylvania tana nan Amurka, baya ga wacce ta kulla da WCCD, ta fuskar sarrafa man kade. Yace idan har aka yi hakan jama’ar jahar zasu ji dadi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:28 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG