Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jahar Naija Na Daukan Matakan Tsuke Bakin Aljihu


Gwamnan Jihar Niger Abubakar Sani Bello yayin ziyarar da ya kawo Sashen Hausa na Muryar Amurka
Gwamnan Jihar Niger Abubakar Sani Bello yayin ziyarar da ya kawo Sashen Hausa na Muryar Amurka

Jahar Naija na daya daga cikin juhohin Najeriya da aka samu sauyin gwamnati a zaben da aka yi shekarar 2015, wacce gwamna Alhaji Abubakar Sani Bello ke jagoranta.

Gwamnatin Sani Bello na gudana ne a karkashin inuwar jam’iyar APC, wacce ta karbe mulkin jahar daga jam’iyar PDP da ta jima ta na mulkar jahar.

Mafi yawan gwamnatocin juhohin Najeriya yanzu haka na fama da rashin kudaden shiga inda su ke ta fadi tashin yadda za su aiwatar da alkawuran da su ka dauka a lokacin yakin neman zabe.

A wasu lokuta ma su kan fuskanci matsalar rashin kudaden biyan albashin ma’aikata ta yadda ya kai ga sai da gwamnatin tarayya ta kai masu dauki.

A wannan hira da su ka yi da gwamna Sani Bello, Ladan Ibrahim Ayawa ya tattauna da shi kan batutuwa da dama yayin wata ziyara da ya kawo ofishin Sashen Hausa na Muryar Amurka inda ya fara da tambayar shi yanayin yadda kudaden shiga ke zuwa jahar ta Naija:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00

XS
SM
MD
LG