Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadan MDD Ya Yi Tur Da Yadda Rikicin Yemen Ke Ta Kanzancewa


Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan rikicin Yemen, ya nuna matukar damuwarsa a yau Alhamis, kan yadda ake kara samun tashin hankali a Yemen

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan rikicin Yemen, ya nuna matukar damuwarsa a yau Alhamis, kan yadda ake kara samun tashin hankali a Yemen, amma kuma ya yi maraba da alkawarin da dakarun da Saudiyya ke jagoranta suka yi, na cewa za su bari a kai kayan agaji a wani muhimmin yanki.
A ranar Talata, Isma’ila Ould Cheikh Ahmed, ya yi Allah wadai da harin makami mai linzami da ‘ya tawayen Houthi suka kai akan Saudiyya, yana mai cewa harin zai iya wargaza shirin zaman lafiyan da aka shimfida a Yemen.
Bayan da ‘yan tawayen suka harba makamin akan wani filin tashin jirage da ke Birnin Riyadh a watan Nuwamba, kasar ta Saudiya ta girke wani shinge a sama da kan teku a Yemen na tsawon wasu makwanni, tana mai cewa daukan wannan mataki ya zama dole domin a dakile safarar makamai da ake yi.
Amma duk da harin na watan Nuwamba, a jiya Laraba dakarun hadin gwiwa da Saudiyan ke jagoranta sun ce, za su bar tashar jiragen ruwa ta Hodeida a bude, har na tsawon kwanaki 30, domin a samu damar aikawa da kayayyakin abinci da sauran kayan agaji.

Facebook Forum

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG