Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadun Philippines Da Norway Sun Mutu a Pakistan


PAKISTAN

A yau lahadi rana ce ta zaman makoki a kasar Pakistan biyo bayan wani hatsarin jirgin sama mai saukar Ungulu da ya hallaka mutane bakwai ciki har da Jakadun wasu kasashe.

Jirgin ya fado ne tare da hallaka mutanen guda bakwai ciki har da jakadun kasar Philippines da Norway a Pakistan da kuma matan jakadun kasar Maleysia da Indonesia hade da ma’aikatan jirgin guda uku.

Hukumomi sun fadi cewa gawarwakin mutanen a yanzu haka suna barikin sojojin sama na Nur Khan a garin Rawalpindi. Jami’ai sun ce jirgin yana dauke da a kalla mutane goma sha bakwai a lokacin da ya fadi a ranar juma’a a tsaunin Naltar a arewacin Pakistan.

Kakakin sojojin kasar Manjo Janar Asim Bajwal ya fada a shafinsa na Twitter cewa jakadun kasar Poland da na Netherlands suna cikin wadanda suka sami tsira a hadarin jingin saman.

‘Yan kungiyar Taliban dai sun ce sune da alhakin kakkabo jirgin mai saukar ungulun da niyyar auna samun Firaministan kasar Nawaz Sharif.

Sai dai Ministan Tsaron kasar ta Pakistan Kawaj Asif yace hatsarin ya faru ne sakamakon matsalar na’ura ba wai saboda harin ‘yan ta’adda ba.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG