Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyar Democrat Ta Kwace Ikon Majalisar Wakilan Amurka


Us Mid term Election
Us Mid term Election

Jam'iyar Democrat ta kwace ikon majalisar wakilan Amurka a zaben rabin wa'adin da aka gudanar jiya Talata yayinda ake kyautata zaton jam'iyar Republican zata ci gaba da rinjaye a majalisar dattijai, a daidai lokacin da ake ci gaba da kirga kuri’u a duk fadin kasar.

An gudanar da zaben ne a kan kujerun majalisar wakilai 435 da wasu kujerun 35 a cikin kujeru 100 na majalisar dattawa da kuma wasu kujerun gwamnonin jihohi 36 cikin jihohin Amurka hamshin. An kuma kada kuri’a kan wadansu batutuwa.

Kusoshin jam’iyar Democrat da dama sun sake lashe zabe da suka hada da Amy Klobuchar ta jihar Minnesota da kuma Elizabeth Warren ta jihar Massachusetts, dukansu ana gani mai yiwuwa su tsaya takarar shugaban kasa a shekara ta dubu biyu da ishirin.

Sai dai ‘yan takarar jam’iyar Democrat a jihohin Indiana da Missouri da kuma North Dakota wadanda ke ci yanzu sun fadi zabe, yayinda ake sauraron sakamakon wani zaben majalisar dattijai mai muhimmanci na jihar Florida tsakanin dan jam’iyar Democrat mai ci Bill Nelson da dan takarar jam’iyar Republican Rick Scott. Dan jam’iyar Republican Ted Cruz ya sha da kyar a fafatawar da suka yi da dan takarar jam’iyar Democrat sabon tauraro a jam’iyar Beto O’Rourke, ya ci gaba da rike kujerar mazabar Kudu maso yammacin Texas.

Da wannan nasarar da jam’iyar Democrat ta samu na kwace ikon majalisar wakilai, bayan samun Karin kujeru 23 da take bukata tayi rinjaye a majalisar, wannan na nufin zasu iya takawa shugaba Donald Trump na jam’iyar Republican birki.

Wannan kuma ya nufin majalisar wakilai zata iya kaddamar da bincike kan gwamnatin Trump.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG